Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa) header
Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa) profile picture

Social Media Activists

Soba, Nigeria
Joined January 2022
Photo by Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa)Photo by Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa)Photo by Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa)Photo by Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa)Photo by Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa)Photo by Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa)Photo by Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa)Photo by Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa)Photo by Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa)Photo by Nasiru Liman Turawa (@LimanTurawa)
I'm deeply grateful and humbled to have been given this opportunity! Thank you for the opportunity, Sen. @ubasanius , CON. Thank you Soba Chairman, Hon. @Molash7879 for the trust & confidence in my abilities. I'm excited to take on this new role and contribute my best efforts...
21
25
2
115
4,276
Nasiru Liman Turawa retweeted
“Shugaba Tinubu ya tattauna da kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos) har aka rage adadin bashin Najeriya a bangaren wutan lantarki zuwa Naira tiriliyan 3.3. A yau, mun biya Naira tiriliyan 1.23 a cikin watanni 18, kuma muna kan tsarin biyan sauran bashin a shekara mai zuwa. Hakan ze warware cikin manyan kalubalen da ake fuskanta a bangaren wutar lantarki a yau, wato bashin da kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos)ke bin Najeriya” ~ Joseph Tegbe, Ministan Wutar Lantarki na Najeriya, ya bayyana haka. #ArewaForAsiwaju #A4A
94
116
8
127
1,756
Nasiru Liman Turawa retweeted
Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ware dala biliyan 3.05 don zuba jari a rayuwar jama’a, da ƙarin dala biliyan 1 don kare marasa ƙarfi. Ga abin da hakan ke nufi ga kowane gida a Najeriya. Manoma da ƙananan ’yan kasuwa: taki, iri, kayan aiki da ƙananan tallafin kuɗi a matakin al’umma. Mutum miliyan 17.6 ne suka amfana a zango na farko. Asibitocin unguwa: ana wadata cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin kare iyaye mata, jarirai da ƙananan yara. ’Yan Najeriya miliyan 40 ne za su amfana. Makarantu: ana inganta makarantun firamare na gwamnati 65,000, ana kuma tallafa wa malamai 500,000. Kusan yara miliyan 30 ne za su ci gajiya. ’Yan gudun hijira: ana sake gina ababen more rayuwa, muhimman ayyuka da hanyoyin dogaro da kai gare su da kuma al’ummomin da ke karɓar su. Iyalai masu rauni: tallafin gaggawa na Naira 40,000 sau ɗaya ga gidaje miliyan 7.6, ta hanyar dijital. Sana’o’i: an horar da ’yan Najeriya 18,510 a sana’o’i 14, aka kuma ba su kayan fara sana’a a jihohi 36 da Abuja. Wannan shi ne shugabanci na gaske. Gyara ababen more rayuwa daga tushe, domin iyalan Najeriya su tsaya da ƙafafunsu. Arewa na tare da Asiwaju. #ArewaforAsiwaju #A4A
89
115
9
128
1,454
Nasiru Liman Turawa retweeted
Kwamitin sulhu na APC ya gana da Badaru bisa umarnin Shugaba Tinubu Kwamitin sulhu na jam'iyyar APC a shiyyar Arewa maso Yamma, ƙarƙashin jagorancin Sanata Abu Ibrahim, ya gana da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, tsohon Ministan Tsaro kuma Darakta-Janar na Arewa for Asiwaju (A4A), Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, a Abuja. Ganawar, wadda aka gudanar a ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2026, ta mayar da hankali kan warware saɓanin cikin gida, ƙarfafa tsarin jam'iyyar da inganta haɗin kai, musamman a jihohin Jigawa, Kano da Katsina. Wannan ganawa na zuwa ne bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga Badaru da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, da su taimaka wajen sasanta ƴan jam'iyyar da ke da saɓani, tare da fifita haɗin kai da muradun jam'iyya. #ArewaforAsiwaju #A4A
79
101
8
113
1,246
Nasiru Liman Turawa retweeted
Sabon littafin Sam Omatseye ya bayyana yadda Tinubu ya taimaka wajen kare takarar Buhari a zaɓen 2015 Wani sabon littafin fitaccen ɗan jarida, Sam Omatseye, ya bayyana yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda a lokacin yake jagorantar jam'iyyar APC a matakin ƙasa, ya yi gaggawar tuntuɓar babban lauya Wole Olanipekun domin taimaka wa kare takarar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a zaɓen 2015. A cewar littafin mai suna From AD to APC: The Evolution of Nigerian Political Parties and the Exploits of One Man (1998–2015), Tinubu ya kira Olanipekun, wanda yake wani aiki a Akure, tare da buƙatarsa da ya garzaya Abuja domin shiga shari'ar da ake yi kan cancantar Buhari na tsayawa takara. Littafin ya bayyana cewa Tinubu ya kuma shirya jirgin sama domin ɗauko lauyan daga Akure zuwa Abuja, domin ya samu halartar zaman kotun da aka shirya yi gabanin zaɓen ranar 28 ga Maris, 2015. A ranar 25 ga Maris, 2015, kotun ta ɗage sauran shari'o'in zuwa watan Afrilu, lamarin da ya sa Buhari ya ci gaba da kasancewa cikin ƴan takarar zaɓen. An bayyana wannan labari ne a babi na 29 na littafin, wanda ya yi nazari kan tarihin jam'iyyun siyasa da tafiyar APC daga shekarar 1998 zuwa 2015. #ArewaForAsiwaju #A4A
81
104
8
122
1,232
Nasiru Liman Turawa retweeted
Maiduguri ta amsa kira, kuma jama'a sun fito ƙwansu da kwarkwatarsu! #ArewaForAsiwaju #A4A
78
98
8
108
2,061
Nasiru Liman Turawa retweeted
“Babu rumfar zaɓe a Instagram, kuma babu rumfar zaɓe a Facebook. Yawan mu'amala a kafafen sada zumunta kaɗai ba zai iya tantance sakamakon zaɓe ba. 'Yan ƙasar da suka fito da kansu suka kaɗa ƙuri'a ne ke yanke hukuncin sakamakon zaɓe.” #ArewaforAsiwaju #A4A
95
124
8
170
5,623
Nasiru Liman Turawa retweeted
“Na san kuna matuƙar damuwa game da halin tsaro. Za mu ci gaba da fuskantar matsalar gaba da gaba. Muna kuma nuna matuƙar girmamawa ga jajirtattun maza da mata na rundunonin sojinmu, waɗanda ke cikin daji da kuma ƙarƙashin tsananin zafin rana suna kare mu.” Kalaman Shugaba Bola Ahmed Tinubu a jawabinsa a Maiduguri, a wajen taron Renewed Hope a Borno. #ArewaforAsiwaju #A4A
87
116
7
130
1,511
Nasiru Liman Turawa retweeted
Hukumar samar da wutar lantarki ta REA ta aiwatar da katafariyar cibiyar samar da lantarki me karfin Megawatt sha biyu (12MW) me amfani da hasken rana (Solar plant) a garin Maiduguri dake jihar Borno. Wannan cibiyar ce take bama Jami’ar Maiduguri da babban Asibitin koyarwa na jami’ar inda hakan ya taimaka wajen zabge kudin wutan labtarki da jami’ar take biya daga N300M zuwa N30M. #ArewaForAsiwaju #A4A
87
116
8
126
1,607
Nasiru Liman Turawa retweeted
“Mai Girma Shugaban Ƙasa, ranka ya daɗe, bari kuma in yi amfani da wannan dama in yaba wa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas (NEDC) bisa dukkan tallafin da ta ba Gwamnatin Jihar Borno da ma dukkan jihohin Arewa maso Gabas ta hannun gwamnatinka. An gina hanyoyi da gadoji masu yawa. Ko a jiyan nan, Mai Girma Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ƙaddamar da shirin samar da motoci masu amfani da wutar lantarki guda 10,000 ga dukkan yankin Arewa maso Gabas, tare da wasu ayyukan da ke kawo sauyi. Saboda haka, ina yaba maka da gaske. Ina kuma tabbatar maka da cewa al'ummar Jihar Borno da ma dukkan jihohin Arewa maso Gabas za su fito ƙwansu da kwarkwatarsu domin zaɓenka a ranar 16 ga watan Janairu, 2027, domin ɗaukakar Allah da kuma amfanin al'umma. Mai Girma Shugaban Ƙasa, baya ga dukkan waɗannan manyan nasarorin ci gaba da aka samu a yankinmu, muna roƙonka cikin girmamawa da ka duba batun dawo da aikin neman man fetur a yankin Kolmani, da kuma gaɓar Tafkin Chadi a yankin Tumbus. Haka kuma, Mai Girma Shugaban Ƙasa, muna fatan ganin an faɗaɗa layin dogo na ƙasa domin ya haɗa dukkan jihohin Arewa maso Gabas. In sha Allah, a zaɓen 2027, al'ummar Jihar Borno, da ma dukkan yankin Arewa maso Gabas, za su zaɓe ka tare da jam'iyyar APC sak, daga sama har ƙasa!” Gwamnan Jihar Borno, @ProfZulum, yayin da yake jawabi a wajen gangamin Sabunta Fata a Borno. #ArewaforAsiwaju #A4A
91
119
8
129
1,854
Nasiru Liman Turawa retweeted
Shugaba Tinubu ya isa Maiduguri don taron yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a jihar Borno. #ArewaforAsiwaju #A4A
93
127
10
146
2,994
At the official book launch of “Gani Fawehinmi and Uba Sani: A Tale Of A Mentor and Mentee”, authored by Mrs. Basirat Fawehinmi-Biobaku, Esq., daughter of the late Chief Gani Fawehinmi, narrated the remarkable deep bond between her family and Governor @ubasanius, CON. She recounted how Governor Uba Sani led other activists, travelled by night bus to Lagos to meet Chief Gani and join the struggle for the restoration of democracy shortly after the annulment of the 1993 presidential election. She further revealed that Governor Uba Sani lived with the Fawehinmi family for over four years, reflecting the depth of the relationship forged during those difficult years of the pro-democracy struggle. Her account offered a compelling reminder of the courage, sacrifice and solidarity that defined Nigeria’s struggle for democracy. #GaniAndUbaSani
4
3
47
Nasiru Liman Turawa retweeted
Shugaban jam'iyyar APC, Nentawe, yayin da yake miƙa tutar jam'iyyar ga dukkan 'yan takarar gwamna na jihohin Arewa maso Gabas. #ArewaforAsiwaju #A4A
96
128
7
150
3,053
Nasiru Liman Turawa retweeted
EARLY MORNING ACTION: I MONITORED OPERATION TSAFTA FOR A HEALTHY KADUNA This morning, I embarked on an inspection of Operation Tsafta activities across major roads in Kaduna to ensure effective service delivery and sustained environmental cleanliness. This is in reinforcement of Governor Uba Sani's commitment to a cleaner, healthier Kaduna State, in line with President Bola Ahmed Tinubu's Renewed Hope Agenda. Hon. Sadiq Mamman Lagos Commissioner for Local Government Affairs, Kaduna State
20
31
15
88
26,998
Nasiru Liman Turawa retweeted
A yau, birnin Maiduguri, wanda tarihinsa ke nuna juriya da kuma yadda al'umma ke iya sake gina rayuwarsu a kowane hali, na tarbar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima. Sun zo ne domin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a filin wasa na El Kanemi Warriors. #ArewaforAsiwaju #A4A
97
123
6
136
1,147
Nasiru Liman Turawa retweeted
Daga Bama zuwa Maiduguri, Borno na ganin aiki a zahiri. Ana sake gina hanyar Bama zuwa Banki da ta Dikwa zuwa Gamboru Ngala da kankare mai ƙarfi, kan Naira biliyan 137, domin sake buɗe hanyoyin kasuwanci zuwa Kamaru da Chadi. NEDC ta kammala hanyoyi a Jere da Mafa, kuma aikin sabuwar Gadar Galtimari zuwa Fori ya kai kashi 80%. Filin jirgin saman Maiduguri ya zama Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Muhammadu Buhari, na farko a Arewa maso Gabas. An kammala tashar wutar lantarki ta gaggawa ta megawat 50, yanzu Maiduguri na samun wuta kusan dare da rana. Ana kuma sake gina Madatsar Ruwa ta Alau kan Naira biliyan 80, domin ruwan sha, kariya daga ambaliya da ban ruwa. Lokacin da ambaliya ta afka wa Maiduguri a 2024, Shugaba Tinubu ya ziyarci garin da kansa. Ya amince da tan 6,000 na abinci, ciki har da tireloli 100 na shinkafa, da kayan agaji na Naira biliyan 1. Mata manoma 1,000 masu rauni sun samu takin zamani kyauta. Jami’ar Maiduguri ce ke kan gaba a Najeriya wajen neman lamunin ɗalibai na NELFUND, da buƙatu 85,050. Tana kuma cikin jami’o’in farko da aka biya, inda ɗalibai 5,839 suka karɓi Naira miliyan 589 a watan Agusta 2024. An ƙaddamar da sababbin manyan makarantu uku a Maiduguri, da Cibiyar Magance Matsalolin Haihuwa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri. Motocin bas, tasi da babura masu ƙafa uku masu amfani da wutar lantarki ma sun fara aiki a Maiduguri. Ba labarin baki ba ne. Aiki ne da kowa ke gani da idonsa. Arewa na tare da Asiwaju. #ArewaforAsiwaju #A4A
99
130
11
141
1,334
Nasiru Liman Turawa retweeted
Dikwa–Gamboru-Ngala Road: Wata babbar dama ta ci gaba ga al’ummar Jihar Borno! Babban aikin wannan hanya zai kawo sauƙi ga zirga-zirgar jama’a, bunƙasa kasuwanci, sauƙaƙa jigilar amfanin gona da buɗe sabbin damammakin tattalin arziki ga mazauna Dikwa, Gamboru-Ngala da sauran al’ummomin da ke yankin. Wannan hanya na da matuƙar muhimmanci wajen farfaɗo da harkokin kasuwanci da noma, tare da inganta rayuwar al’ummar yankin. Yabo ya tabbata ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa wannan yunƙuri na samar da ababen more rayuwa da za su amfani al’umma tare da bunƙasa ci gaban ƙasa. Aiki ne mai muhimmanci, wanda tasirinsa zai bayyana a rayuwar jama’a da tattalin arzikin yankin. #ArewaforAsiwaju #A4A
93
127
9
136
3,072
Nasiru Liman Turawa retweeted
“Ka taɓa maigidana, ni kuma zan tunkare ka.” Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya sake jaddada matsayinsa na biyayya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a lokacin da yake jawabi a Maiduguri a jiya. #ArewaforAsiwaju #A4A
97
118
7
131
2,664
Nasiru Liman Turawa retweeted
Dikwa- Borno State Makarantar Sakandare ta Gwamnati ta Jeka Ka Dawo da ke Dikwa, Jihar Borno, ta samu gyare-gyare da inganta muhallinta a ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. An sabunta gine-ginen makarantar tare da samar da sababbin kujeru da tebura a azuzuwa domin inganta yanayin koyarwa da koyo. Bidiyon ya nuna yadda azuzuwan makarantar suka inganta, tare da yadda malamai ke gudanar da darussa, ciki har da koyar da lissafi. Haka kuma, shugaban makarantar, Malam Muhammed Modu, ya yi ƙarin bayani kan makarantar da sauye-sauyen da aka samu. Wannan na daga cikin ayyukan da gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiwatarwa domin inganta kayayyakin more rayuwa a makarantu da samar da yanayin da zai taimaka wa ɗalibai wajen samun ingantaccen ilimi. #ArewaforAsiwaju #A4A
92
123
7
135
1,741
Nasiru Liman Turawa retweeted
Arewa ta ga aiki a zahiri. Tun daga 2023, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tana aiwatar da manyan ayyuka a jihohin Arewa. Ga kaɗan daga cikinsu. An kammala babban bututun iskar gas na AKK daga Ajaokuta zuwa Kaduna da Kano, domin samar da gas ga masana’antu da wutar lantarki a Arewa. Za a ƙaddamar da layin dogo na Kaduna zuwa Kano ranar 3 ga Disamba, bayan gwajin da aka yi cikin nasara. Hanyar Abuja zuwa Kano ma, an gama kilomita 118 na farko. An kuma fara gina babbar hanyar Sakkwato zuwa Badagry. Manoman alkama sama da 386,000, galibinsu a Arewa, sun samu tallafin iri da taki. An kuma kafa Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo, da hukumomin raya Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya. An kafa sababbin jami’o’in tarayya a Kano da Kaduna domin matasanmu. A Maiduguri kuma, ana sake gina madatsar ruwa ta Alau da Naira biliyan 80. Wannan ba labari ba ne. Aiki ne da ake gani. Arewa na tare da Asiwaju. #ArewaforAsiwaju #A4A
83
117
7
126
970
Nasiru Liman Turawa retweeted
Saboda ɗumbin jama'ar da suka fito, an gudanar da tattaki domin isa fadar Gabasawan Katsina, Hakimin Dutsi, a lokacin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko 2027 a ƙaramar hukumar Dutsi. #ArewaforAsiwaju #A4A
92
115
6
127
2,107