BBC Hausa - Fiye da shekara 60 na labaran duniya da rahotannin da suka shafi rayuwarku

London
Joined December 2008
Kalli yadda girgizar ƙasa mai maki bakwai ta faru a Tibet. Girgizar ƙasar ta yi sanadin mutuwar mutum 16, kuma hukumomi sun ayyana dokar ta ɓaci a yankin.
2,788
Kwamitin, wanda ya ƙunshi manyan ƴan siyasa da tsofaffin masu riƙe da muƙaman gwamnati, zai kasance cibiyar tsara dabaru da daidaita ayyukan yaƙin neman zaɓen Peter Obi da Kwankwaso Ƙarin bayani: bbc.in/3TWBnJN
1
1
6
3,805
Masu hasashe sun sanya ƴan wasan gefe na Sifaniya, Lamine Yamal, da kyaftin ɗin Ingila, Harry Kane, da ɗan wasan gaban Real Madrid a matsayin waɗanda ke kan gaba a takarar lashe babbar kyautar. Karin bayani - bbc.in/47Z9Afb
7
6
60
5,466
Ministan lafiyar Najeriya ya tabbatar da cewa an fice da matar da ke ɗauke da cutar Ebola daga Najeriya zuwa Switzerland tare da mijinta inda za ta ci gaba da samun kulawa. Ya kuma ce tana samun sauƙi sannan sun gano wasu mutum 53 da ake tunanin matar ta yi muʼamala da su.
2
19
4,845
Ƴanbindiga sun kai hari ƙauyen Binnari da ke ƙaramar hukumar Karim Lamido, jim kaɗan bayan sallar Juma'a, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi, tare da ƙona shaguna da babura. Ƙarin bayani - bbc.in/4ke427B
15
5,021
A farkon kakar wasa ta bana Barca ta riƙa taka rawar gani inda ta doke wasu ƙungiyoyi, sai kwatsam PSG da Real Madrid suka taka mata burki a Champions League da La Liga.
3
1
70
5,484
A wani sakamako da ya bai wa mutane da dama mamaki, wata ƙungiyar ɗalibai masu zanga-zangar neman sauyi ce ta lashe babban zaɓen ƙasar Serbia, inda ta doke tsohon shugaban ƙasar Aleksandar Vucic, wanda ya shafe shekaru 14 yana mulki. Ƙarin bayani - bbc.in/3W5hKji
1
1
50
5,474
A ranar 3 ga Nuwamba, Amurkawa za su zaɓi membobin Majalisar Dokokin Amurka , wadda ta ƙunshi ɓangarori biyu: Majalisar Wakilai da kuma Majalisar Dattawa Karin bayani: bbc.in/4z8f1nE
1
2
28
4,803
Yaƙin da Isra'ila da Amurka suka ƙaddamar kan Iran ya janyo hauhawar farashin makamashi a kasuwannin duniya, kuma babu wata alama da ke nuna cewa zai ƙare nan kusa Karin bayani: bbc.in/48d52ld
1
4
58
4,443
Tsohon mai horar da yan wasan Newcastle Eddie Howe, da yanzu ba shi da aiki, zai iya kasancewa a shirye wajen tattaunawa da Manchester United idan old Trafford ɗin suka raba gari da Michael Carrick Karin bayani: bbc.in/4inv9KZ
1
18
3,568
Yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, ɗaya daga cikin tambayoyin da ke janyo ce-ce-ku-ce a siyasar Najeriya ita ce ko jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, zai iya raba wa Atiku Abubakar ƙuri'un Arewacin ƙasar? Karin bayani: bbc.in/4kg0mCn
16
3
2
98
6,010
Real Madrid ta doke Barcelona a Camp Nou a karawarsu ta faro a kakar wasan 2026/2027. Mbappe ne ya zura ƙwallo biyu yayin da Raphinha ya ci wa Barcelona ɗaya. Yaya kuka ga wasan?
1
4
109
6,342
Ministan lafiya na Najeriya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya yi wa BBC ƙarin bayani kan halin da ake ciki a yanzu bayan shigowar cutar Ebola ƙasar. Ya kuma bayyana matakan da suke ɗauka domin yaƙar cutar. 🎥 - Abba Auwalu
5
38
320
21,640
A ranar Lahadi ne Bornemouth ta lallasa Man United 3-0, kwanaki kaɗan bayan Como ta lallasa ta 4-1 a Champions League. A halin yanzu ita ce ta 16 a teburin Premier League.
3
4
34
7,352
Kalli yadda wasu ʼyan fashi suka buɗe wuta a wani coci yayin da ake janaʼiza a ciki, suka kashe wasu mutane. Lamarin ya faru ne a ƙasar Jordan.
1
2
18
7,904
A yau Lahadi za a fafata a wasan El Clasico na farko a kakar wasan 2026/2027 inda Barca ke saman teburin La Liga yayin da Madrid ke ta uku. Wannan ne El Clasico na farko da Mourinho zai jagoranci Madrid tun bayan 2013, kuma Mbappe da Yamal za du kece raini kwana ɗaya kafin bikin Ballon d’Or.
1
5
73
8,034
Kakakin Majalisar Dokokin Iran kuma babban mai tattaunawar ƙasar ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar kafin fara zaman majalisar a ranar Lahadi. Ƙarin bayani - trib.al/oc7YLIO
2
10
142
14,459
Ƙungiyar da ake kira “October Council”, wadda iyalan waɗanda harin Hamas na ranar 7 ga Oktoban 2023 ya shafa suka kafa, ce ta shirya zanga-zangar. Ƙarin bayani - trib.al/tMa4yFs
3
9
116
9,491
Tun bayan fara sabon zangon karatu a ranar 1 ga Oktoban 2026, hukumomin Burkina Faso suka fara wani tsari na "kawar da tasirin mulkin mallaka" daga tarihin da ake koyarwa a tsarin iliminsu Karin bayani: bbc.in/4i5Rkqi
2
48
8,278